Mayaƙan Al-Shabab sun ƙaddamar da Yaƙi a Yankin Awdheegle da ke Kuɗancin Somalia

 

Mayaƙan Al-Shabab sun ƙaddamar da wani yaƙi a safiyar nan a yankin Awdheegle da le gundumar Lower Shabelle a kudancin Somaliya.

Maharan sun kai hare-hare ta fuskoki da yawa na birnin, yayin da dakarun gwamnati ke ci gaba da yunkurin kare su.

Mutanen da ke yankin Awdheegle sun shaida wa BBC cewa faɗan ya ɓarke ne da misalin ƙarfe huɗu na safiya kuma an shafe awanni ana gwabzawa.

Mazauna yankin sun ce sun riƙa jin harbin bindiga ta ko wanne bangare da ke yaƙi da juna.

Gwamnan gundumar Lower Shabelle, Mohamed Ibrahim Barre, ya shaida wa BBC dakarun gwamnati sun durƙusar da gungun maharan, inda ya ce duka ɓangarorin sun yi rashin mayaƙa, amma har yanzu ba su da cikakkun bayanai kan abin da ya faru.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com