Alamomin Kansar Mama

 

Mutane suna jin an ce kansa ko cutar Daji, kowa yasan cuta ce da ake shan wuya kuma ba a warkewa idan ana fama da ita.

Amma tun karshen shekarun 1970, adadin mutanen da ke tsira daga wannan cuta ke ninkawa sau uku, dalili kuma shi ne da yawan marasa lafiyar akan iya cetonsu daga cutar da zarar an gano suna da ita a kan lokaci.

Matsalar ita ce ba mu fiye bai wa likitoci muhimmanci ba, domin kuwa sukan iya gano alamun cutar tun da wuri matuƙar an tuntube su a kan lokaci.

A cewar wani bincike da cibiyar binciken kansa ta Birtaniya ta yi, an gwada rabin mutanen Birtaniya an gano wasu na ɗauke da alamun cutar amma kuma kashi biyu ne kacal ake zargin sun kamu da ita.

Katrina Whittaker, wata mai bincike a Jami’ar Landan, wadda kuma ita ce ta jagoranci wannan binciken, ta ce: “bai kamata mutane su riƙa tsammanin muna son sanya musu fargaba da tsoro ba ne a ransu, ya kamata mutane su riƙa sanin yanayin da suke ciki na lafiya, bai kamata su riƙa jin kunyar zuwa ganin likita ba.”

Ga wasu alamu 8 da an ji su an san cutar kansa ta samu:

1- Ramewa mara dlili

2- Yawan Zazzaɓi mara ƙaƙƙautawa

3- Yawan laulayi

4- Sauyin launin fata ga masu kansar fata

5- Yawan ciwon ciki ga masu kansan da ke alka da ciki (Hanji, Tumbi, mahaifa, ƙoda, hanta da sauransu)

6- Ƙurjin da ke komawa da ke gyambo

7- Zubar da Jini ga masu kansar jini ko kansar bakin mahaifa

8-Tari maras warkewa ga masu kansar huhu

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com