Babban Kwamitin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya ta Sanar da Ranar Nadin Sabuwar Darakta Janar
Tsohuwar Ministar kudi a Najeriya, da yiyuwar ta kasance sabuwar Darakta-Janar na WTO.
Hukumar ta sanar da sabon nadin Darakta-Janar din zai gudana ranar 15 ga watan Fabrairu.
A baya, an bayyana tsohuwar ministar a matsayin ‘yar takara tilo da ta fito neman kujerar.
Babban Kwamitin Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, WTO, ya ce zai duba yiwuwar nada Darakta-Janar na gaba mako mai zuwa ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
Ku tuna cewa tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, ita ce ‘yar takara tilo da ta bayyana a wannan matsayi, biyo bayan sauka daga wani dan takarar wanda ya kasance Minista a Koriya a makon da ya gabata.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa mai taken, ‘WTO General Council da za ta yi la’akari da nadin Darakta-Janar na gaba’ da ta wallafa a shafinta na intanet a ranar Talata, ta ce za a gudanar da taro na musamman na Babban Kwamishinanta a ranar 15 ga Fabrairu.
“Babban Kwamitin WTO zai yi taro na musamman a ranar 15 ga Fabrairu da misalin karfe 3:00 na yamma lokacin Geneva don yin la’akari da nadin Darakta-Janar na gaba. Taron zai gudana ne cikin tsari na kamala,” sanarwar ta kara da cewa.