Hukumar Kwastam ta Magantu Kan kaɗe Matashi a Garin Jibiya

 

Hukumar kwastam ta Najeriya ta yi bayani kan batun kashe wani matashi da aka yi a garin Jibiya na jihar Katsina, bayan da aka zargi jami’anta da bin mai motar da gudu a cikin gari.

A makon da ya gabata ne wasu rahotanni suka ce jami’an hukumar ta kwastam sun bi wani mai mota ƙirar J5 da nufin kama shi, lamarin da ya sanya ya kaɗe wani matashi, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

A cikin wata sanarwa da hukumar kwastam ta Najeriya ta fitar, yau Litinin ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar na ƙasa, Abdullahi Maiwada, hukumar ta ce yana da kyau ta fayyace wa al’umma cewa “ba jami’anmu ne suka tuƙa motar ƙirar J5 ba kuma ba su kama motar ba.”

Sanarwar ta ƙara da cewa binciken da hukumar ta gabatar ya nuna cewa direban J5 ɗin na ɗauke ne da waken soya, kuma tuni aka kama shi inda yake hannun jami’an ƴansanda.

Sai dai sanarwar ta ce hukumar ta kwastam na jajanta wa iyalan mamacin.

Rahotannin da kafafen yaɗa labaru suka fitar sun ce a ranar Asabar ne wani matashi mai suna Muhsin Ibrahim mai shekara 14 da haihuwa ya rasa ransa bayan da wata mota ƙirar J5 ta kaɗe shi a cikin garin Jibiya na jihar Katsina, wadda ake zargin wasu jami’an kwastam ne suka biyo shi.

Wannan ba shi ne karon farko da ake zargin jami’an hukumar kwastam da haddasa hatsari ba a garin na Jibiya wanda ke maƙwaftaka da Jamhuriyar Nijar mai maƙwaftaka da Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com