Hukumar Kwastam za ta ƙwace Jirage na ɗaiɗaikun Jama’a 29 a Najeriya
Hukumar kwastam a Najeriya ta yi barazanar ƙwace wasu jirage na ɗaiɗaikun jama’a 29 waɗanda masu su ba su biya kudaden fito ba.
A wani rahoto da ta fitar kakakin hukumar Joseph Attah, ya ce idan ba su bayyana kansu domin biyan kuɗaɗen da ake bin su to za a ƙwace jiragen cikin kwanaki 14.
A ranar 31 ga watan Mayu kwastam ta sanar da shirinta na soma bincikar irin wadannan jirage a ƙasar.
An gudanar da binciken ne tsakanin 7 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Agusta.
Attah ya ce a lokacin binciken mamalakan irin wadannan jirage mutum 86 sun hallara da gabatar da takardun da ake bukata.
Ya ce cikin 57 wadanda ake kasuwanci da su ne, sannan 29 ba su cika ka’idoji ba.