Labaran ƙarya da ake Yaɗawa a Kan Alƙalan da ke Jagorantar Shari’ar Zaɓen Shugaban Najeriya

 

Alƙalai na can suna yanke hukunci a kan shari’ar da ke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Jam’iyya uku wato PDP da LP da APM ne ke ci gaba da ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

Shari’ar na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da yaɗa labarai daban-daban a shafukan sada zumunta, inda ake zantuka game da alƙalan da ke jagorantar shari’ar.

Jami’an yaƙi da labaran ƙarya na BBC sun duba wasu daga cikin waɗannan zarge-zarge da ake yaɗawa.

Iƙirarin ƙarya kan janyewar alƙali

A watan Yuli, wani shafin intanet mallakar wata mujallar mai suna Igbo Times ta wallafa wani labari da ke zargin cewa ɗaya daga cikin alƙalai biyar da ke jagorantar shari’ar Boloukuoromo M. Ugo, ya janye daga ci gaba da yanke hukunci bisa dalilai masu nasaba da “durƙusar da dimokraɗiyya”.

Shafin ya ta’allaƙa kalaman da ya ce Mai shari’a Ugo ne ya yi su.

Rahoton shafin ya kuma ce Mai shari’a Ugo ya yi wani kalami na cewa, “game da wannan lamari duk wani matakin goyawa gwamnati baya daidai yae da haifar da cikas ga dimokraɗiyyar Najeriya”, a kan haka ba zai tsuke bakinsa ya yi shiru ba”.

Haka ma mujallar ta Igbo ta yi zargin cewa alƙalin ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta nemi ya mara wa ɗan takararta baya a shari’ar.

Labarin dai ba gaskiya ba ne, domin Mai shairi’a Ugo bai sauka daga matsayinsa na ɗaya daga alƙalan biyar da za su yanke hukunci ba, kuma babu wata hujja ƙarara game da zargin na mujalar Igbo Times.

Shafin ya watsa labarin a sauran shafukansa sada zumunta, inda masu amfani da kafofin suka riƙa yaɗa shi cikin su har da Charles Oputa da aka fi sani da Charly Boy, wanda ya yaɗa shi ga masu bin shafinsa fiye da 350,000.

Sai dai daga baya, mujallar ta cire labarin amma har yanzu akwai shi a shafin Charly Boy a dandalin X da aka sani da Tuwita, da sauran mabiya shafukan sada zumunta.

Ita kan ta Igbo Times ba ta cire labarin daga shafinta na X ba.

Zargin Babban alƙalin kotun Najeriya ya gana da Tinubu a Landan

A watan Maris kuma wata jaridar da ake wallafawa a intanet mai suna People Gazette, ta ruwaito cewa alƙalin alƙalan Najeriya ya yi shigar burtu tamkar wani mai fama da lalura ta musamman, inda ya gana da Tinubu a matsayinsa na zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

Ta yi iƙirarin cewa mutanen biyu sun tattauna ‘wasu batutuwan da ake sa ran za a iya tado wa a shari’ar da ke ƙalubalantar sa a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa”.

An samu shafukan intanet da dama a Najeriya da suka watsa wannan labarin da ba a tabbatar da shi ba, har ma aka rinƙa saka hotunan da ke nuna ana tura alkalin alƙalan a keken marasa lafiya zuwa harabar tarbar baƙi na filin jirgin.

Kotun ƙolin Najeriya ta bayyana cewa lallai babban alƙalin ya yi bulaguro zuwa Landan, amma ya je ne domin a duba lafiyarsa, kuma bai yi wata ganawa da da Tinubu a can ba.

Kuma babu wata hujjar da ke nuna cewa mai shari’a Olukayode Ariwoola ya gana da Tinubu a yayin wannan ziyara da ya kai Landan.

Labaran ƙarya game da ranar yanke hukunci

A watan Satumba, an samu wasu magoya bayan jam’iyyar LP da ke amfani da shafukan sada zumunta da suka fara watsa jerin iƙirari da ke cewa an sa 16 ga watan Satumba a matsayin ranar yanke hukunci.

Wannan labarin ya zama abin tattauna tsawon makonni kafin daga baya a gane na ƙanzon kurege ne.

Lokacin da aka ba da sanarwar cewa 6 ga watan Satumba ce ranar da za a ci gaba da sauraren ƙarar da ‘yan takarar jam’iyyun uku suka shigar ba kamar yadda masu watsa labaran suka ambata ba.

Zargin dakatar da kotuna

A watan Yuli, jaridar yanar gizo ta Igbo Times ta wallafa wani labarin ƙarya shi ma da ke cewa Shugaban ƙasa Tinubu ya dakatar da “dukan kotuna a Najeriya a bisa dalilan fargabar rashn cancantar su”.

Igbo Times ba ta kuma bayar da wata hujja akan wannan zargi ba wanda tun a wancan lokaci masu tantance labaran ƙarya suka yi bayyana labarin a matsayin na ƙanzon kurege. Amma har wannan lokaci labarin na nan a shafin mujallar.

Ƙarin labaran da ke karkatar da jama’a

Sanarwar da kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta fitar shi ma ya haifar da masu shafukan sada zumunta taka rawa wajen fitowar wasu sabbin labarai masu karkatar da hankalin jama’a.

Wani mai amfani da shafin Twitter da ya yi amfani da taken @MissPearls ya yi zargin shugaba Tinubu “na wani shiri na yin tafiya wata ƙasar waje” inda ya ke karkatar da hankalin cewa “an tsara masa barin ƙasar da sunan halartar wani taro”

Har ila yau, tun a watan Afirilu aka sanar da shirin tafiyar shugaban Najeriyar zuwa Indiya bayan da Firaminitan ƙasar Narendra Modi ya gayyace shi ya halarci taron ƙolin ƙasashen masu ƙarfin tattalin arziki na G20 da zai gudana a ƙasar a rana 9 da 10 ga watan Satumba.

Yi wa ‘yan’uwan alƙalin barazana

Baya ga sauran kalamai da rahotannin ƙarya da suka shafi yanke hukuncin, magoya bayan wasu jam’ijyyu sun watsa saƙonni da hotunan da ke barazana da aka ce wai daga iyalan alƙalan su ke da ke nuna ana razanar da su daidai lokacin da ke daf da soma shari’ar.

Galibin magoya bayan jam’iyyun sun matsa ƙaimi wajen baza waɗannan a shafukansu na sada zumunta inda su ke saka alamar hastag mai nuna cewa jama’a na lura da yadda shari’ar ke gudana #AllEyesOntheJudiciary.

Alƙalan dai sun soma jagorantar wannan shari’ar da ‘yan takarar jam’iyyu uku suka shigar a ranar Larabar nan 6 ga watan Satumba 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com