ƙalubalantar Nasarar Tinubu: Kotu ta Kori ɗaya Daga Cikin ƙorafe-ƙorafen Jam’iyyar APM

 

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya ta kori ƙarar jam’iyyar APM wadda ke ƙalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu, na jam’iyyar APC.

Mai shari’a Haruna Tsammani da ya jagoranci alƙalan kotun biyar, shi ne ya karanto hukuncin wanda ya ce hukumar zaɓe ta yi daidai da ta tabbatar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.

Shi ne hukunci na farko a cikin hukunce-hukunce guda uku da kotun za ta yanke yayin zamanta na yau Laraba.

Jam’iyyar APM ce ta shigar ƙarar a kan Bola Ahmed Tinubu da Hukumar Zaɓe ta INEC da kuma Kabiru Masari, mutumin da ɗan takarar APC a wancan lokaci ya fara gabatar wa INEC a matsayin wanda ke mara masa baya kafin ya sauya shi da Kashim Shettima.

Tun farko, an shaida wa kotun cewa masu ƙarar, ba su hallara a kotun ba.

Jam’iyyar tana ƙalubalantar ɗaukar Kashim settima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa ne. Tana cewa maye shi a gurbin Kabiru Masari, ya saɓa wa tsarin mulki.

Mai shari’a Tsammani ya ce ƙarar da APM ta shigar, batu ne da ya shafi harkokin da ake la’akari da su kafin zaɓe.

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta fara zama don gabatar da hukunci a kan ƙorafe-ƙorafen da wasu ‘yan takara suka shigar mata, bayan zaɓen watan Fabrairun 2023.

Jami’an tsaron da aka jibge tun da sanyin safiya, sun datse titin da ke zuwa harabar kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, inda ake zaman.

Kotun mai alƙali biyar a Abuja ta shafe watanni tana karɓar bahasi da kuma sauraron muhawara game da ƙorafe-ƙorafen maguɗi da jam’iyyun adawa na PDP da LP suka yi.

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaɓen Najeriya, inda ya samu yawan ƙuri’un da suka kai kashi 37 cikin 100 a zaɓen ranar 25 watan Fabrairu. Abin da ya ba shi galaba a kan Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar LP.

Wannan, ba shi ne hukuncin ƙarshe da mai yiwuwa za a iya samu game da zaɓen ba, masana shari’a na cewa jam’iyyu na iya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli wadda za ta yanke hukunci na ƙarshe.

An ga manyan jami’an gwamnatin Najeriya ciki har da mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje da gwamnonin jam’iyyar, duk sun hallara a kotun.

Haka zalika, akwai wasu gwamnonin adawa kamar na jihar Bauchi, Bala Mohammed a kotun da shugaban PDP, Umar Iliya Damagum.

Mai shari’a Haruna Tsammani tare da sauran alƙalan kotun sun fito inda suka zauna don fara gabatar da hukunci.

Livy Uzogwu shi ne wanda ke jagorantar lauyoyin jam’iyar LP, inda ya gabatar da kansa.

Ƙarar Atiku

Akawun kotu ya ci gaba inda ya kira ƙarar da Atiku Abubakar na PDP ya shigar da waɗanda ake ƙara.

Barista Chris Uche ne ke wakiltar masu ƙara na ɓangaren Atiku Abubakar.

Ya fara gabatar da dalilai da suka nuna cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima bai cancanta ya tsaya takara ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com