Ya Kamata ƙasata ta Taƙaita Yawan Haihuwa – Shugaban Masar

 

Shugaban ƙasar Masar Abdul Fattah al-Sisi ya ce ƙasarsa na buƙatar rage yawan haihuwa domin kauce wa manyan matsalolin da ke tunkarar ƙasar.

Shugaba Sisi ya ce ya kamata ƙasar ta taƙaita yawan haihuwa zuwa 400,000 a shekara, maimakon fiye da haihuwa miliyan biyu da ake samu a ƙasar kowace shekara, domin samun damar yi wa ‘yan ƙasar ayyukan more rayuwa da samun ayyukan yi.

Mista al-Sisi ya yi watsi da maganar da ministan lafiyar ƙasar ya yi, cewa samun ‘ya’ya na daga cikin ‘yancin ɗan’adam.

“Wane ‘yanci, bayan suna janyo wa mutane ƙarin wahala? a ƙarshe duka al’umma ne da ƙasarmu za su sha wahalar”.

“Ya kamata mu san yadda za mu yi da wannan ‘yancin, in ba haka ba kuwa mu ƙirƙirar wa kawunanmu wahala”.

Ya ƙara da cewa Ƙasarsa za ta koikoyi China kan tsarin haihuwar ɗa ɗaya ga kowaɗanne ma’aurata, “tun da dai Chinan ta samu nasarar rage yawan al’ummarta”.

Daga shekarar 2000, yawan al’ummar Masar ya ƙaru da miliyan 40, inda a yanzu yawan al’ummar ƙasar ya kai miiyan 150, kamar yadda alƙaluman hukumomin ƙasar suka nuna.

Mista al-Sisi ya kuma shawarci sauran ƙasashen Afirka su rungumi matakin rage yawan jama’a, kasancewar nahiyar na fama da ƙarancin abubuwan da jama’ar ke buƙata domin su rayu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com