Kasar Larabawa: ta Haramta Kashe Mata Masu Jawo Abin Kunya
Gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ƙara tsaurara hukunci kan kisan da dangi ke yi wa mata a ƙasar a yunƙurin yin garambawul ga dokokin ƙasar.
Gwamnatin ƙasar ta ce za ta soke dokar da ta bai wa alƙalai damar yanke hukunci mai sauƙi kan irin wannan kisan.
Akasari, ana kashe matan ne sakamakon zargin da ake yi musu na janyo abin kunya ga zuri’a ko kuma danginsu baki daya.
Daga yanzu, za a riƙa hukunta waɗanda suka kashe irin waɗannan mata daidai da irin hukuncin da aka yanke wa waɗanda suka aikata kisa, in ji gwamnatin ƙasar.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’Adam sun ce a duk shekara ana kashe dubban mata a faɗin duniya sakamakon zargin da ake yi musu na jawo wa danginsu abin kunya.
Read Also:
Ƙungiyoyin sun lissafo jima’i ba tare da aure ba a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suke sa ana kashe matan.
Kamfanin dillancin labarai na WAM ya ruwaito cewa saka dokoki masu tsauri irin waɗannan da Daular Larabawan ke yi na nuna aniyarta ta kare haƙƙoƙin mata.
Sauya waɗannan dokoki na ɗaya daga cikin sauye-sauyen da Shugaban Ƙasar Sheik Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya amince da su a ranar Asabar.
Wani sauyin da aka yi kuma shi ne batun barin baƙi mazauna ƙasar su zaɓi irin tsarin da suke so na rabon gado da kuma rubuta wasiyya.
WAM ya ce wannan matakin zai taimaka wa ƙasar wurin samun tattalin arziƙi mai ƙarfi daga masu zuba jari.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan Amurka ta shirya Daular Larabawan da Isra’ila domin yin ƙawance irin na difilomasiya.
Ana sa ran ƙawancen da aka ƙulla zai taimaka wurin jawo masu yawon buɗe ido zuwa ƙasar domin shaƙatawa ko kuma kasuwanci