Yadda Lagos ta Tafka Asarar Sama da Naira Biliyan 400 Saboda Zanga-Zangar EndSars
Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ta yi asarar kimanin sama da dalar Amurka biliyan ɗaya sakamakon rikicin da ya ɓarke a jihar, biyo bayan zanga-zangar EndSars da ake yi.
A hira da BBC, Shugaban Cibiyar Kasuwanci Ta Legas, Muda Yusuf, ya ce duk da cewa ba a gama tattara alƙaluma kan ƙiyasin asarar da wannan tarzoma ta jawo ba, amma an yi asarar sama da dalar Amurka biliyan ɗaya, kimanin kuɗin Najeriya naira biliyan biliyan 400 kenan.
A ranar Laraba ne dai tarzomar da aka yi a jihar ta Legas ɗin ta fi ƙamari inda aka lalata gidaje da ofisoshi da masana’antu da wuraren aiki.
Duk da jami’an tsaron da aka jibge a jihar domin shawo kan tarzomar, an ɗauki lokaci mai tsawo ana ƙone-ƙone a cikin jihar.
“An shafe kusan mako biyu da fara tagayyara tattalin arziƙin Legas da na Najeriya sakamakon wannan zanga-zangar, ganin cewa Legas ita ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya,” in ji shi.
A cewarsa, idan aka samu tsaiko na tattalin arziƙi a Legas, tasirin da abin zai yi ga Najeriya yana da yawa, kuma zai ɗauki lokaci mai tsawo kafin a farfaɗo.
“Gwamnati ta yi asara, kamfanoni masu zaman kansu sun yi asara, haka masu zuba jari, an yi asarar sama da ƙadarori 100 kuma ba wai ƙanana ba,”, a cewarsa. Kadarorin dai sun haɗa da ofisoshi da kamfanoni da masana’antu da sauransu.
Wane tasiri wannan asarar za ta yi ga tattalin arziƙin Legas da Najeriya
Mista Muda Yusuf ya bayyana cewa wannan asarar ta mayar da hannun agogo baya ta fuskar ci gaban da ƙasar ke samu bayan ƙasar ta fara farfaɗowa daga asarar da aka samu a lokacin annobar korona.
“An samu raguwar tattalin arziƙi da kashi 6.1 a watanni shidan farko na wannan shekara, yanzu kuma ga wata sabuwar girgiza an sake samu, wannan yasa ake ƙara mayar da hannun agogo baya.
“An samu koma baya a ɓangaren zuba jari da farfaɗo da tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.”
Read Also:
A cewarsa, sanadiyar lalata wasu kamfanoni da masana’antu, hakan zai jawo mutane da dama su rasa ayyukansu, ya kuma ce akwai kamfanoni da dama da cikin shekara ɗaya ko biyu ba za su iya farfaɗowa ba.
“Kadarori da dama da aka lalata a ƙarƙashin tsarin inshora suke wanda hakan zai ƙara matsin lamba ga kamfanonin bayar da inshora.
Girman asarar da aka yi a Legas
A tattaunawar da BBC ta yi da Muda Yusuf, ya bayyana cewa an lalata da kuma ƙona wurare a jihar ta Legas sama da 100.
Ga kaɗan daga cikin wuraren da muka tattaro da aka lalata ko kuma ƙonawa.
Hedikwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA
Gidan Oba na Legas
Gidan talabijin na TVC
Gidan mahaifiyar Gwamna Sanwo-Olu
Tashar mota ta Oyingbo
Otel din Orientel
Ofishin hukumar Road Safety da VIO
Babbar Kotun da ke Igbosere
Manyan kantunan sayar da kayayyaki na Shoprite da Spar
Ofishin jaridar The Nation
Wasu daga cikin ofisoshin ‘yan sandan da aka lalata
Ofishin ‘yan sanda na Idimu
Igando
Layeni
Denton
Ilenbe Hausa
Ajah
Akwai kuma ofishin ‘yan sanda na Amukoko
Akwai ofishin rusashiyar rundunar SARS a Ajegunle.
Wannan layi ne
Wane mataki aka ɗauka na cike giɓin asarar da aka tafka a Legas?
Mista Muda Yusuf ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani mataki a ƙasa da za a ce anɗauka na cike giɓin irin wannan asarar ganin cewa har yanzu mutane na cikin ruɗani da kaɗuwa duba da irin girman asarar da aka tafka.
Ya ce kamfanonin da suke da inshora ne kaɗai a yanzu za su ɗan samu sauƙi wurin farfadowa, amma waɗanda ba su da inshora hakan na nufin sai dai su haƙura ko kuma su san yadda za su yi su farfaɗo da kansu.
Ya ce a ɓangaren gwamnati, sake gina waɗannan kadarorin a wurin ta yana da wahala matuƙa duba yadda tattalin arziƙi ke tafiya da kuma yanayin samun harajinta ya ragu.
Ya ce da kudin da aka yi asara, ya isa a yi wa mutane ayyuka da suka shafi asibitoci da tituna da gidaje.