Jahar Legas ta Kori Wasu ‘Yan sanda Daga Aiki

Hukumar ‘yan sandan jihar Legas ta kori jami’anta guda 10 saboda aikata laifuka daban-daban.

Laifukan da suka aikata sun hada da karbar rashawa, amfani da matsayinsu wurin yin zalunci da sauransu.

Kakakin hukumar, SP Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da hakan a wata takarda da ya saka hannu ranar Laraba Hukumar ‘yan sanda ta jihar Legas ta bayyana korar jami’an ‘yan sanda guda 10 a ranar Laraba da tayi, saboda sun aikata laifuka daban-daban.

Kakakin hukumar, SP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya sa hannu, kuma ya gabatar wa manema labarai a jihar Legas.

Kamar yadda kakakin yace, anyi korar ne don ladabtar da ‘yan sandar jihar, Daily Nigerian ta wallafa.

Adejobi ya ce hukumar ta binciki ‘yan sanda 81 da suka yi laifuka daban-daban, tsakanin watan Oktoban 2019 zuwa watan Oktoban 2020. A cewarsa, laifukan sun hada da kisa, amfani da matsayinsu su yi zalunci, rashawa da kuma rashin bin dokokin aikin.

Ya kara da cewa, hukumar ta kori jami’ai 10, ta rage matsayin 18 sannan ta bai wa sauran wasikun jan kunne.

Ya shawarci jama’a da su tabbatar sun kai karar duk wani laifi da suka ga ‘yan sandan sun yi, don hakan ne kadai zai kawo gyara a kasar nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here