An Kara Samu ɓullowar Sabuwar Cuta a Nigeria

Wata bakuwar cuta ta bulla a garin Okpeilo-Otukpa da ke jihar Benue.

An tattaro cewa cutar ta halaka mutane 17 cikin yan kwanaki yayinda sauran mutane da suka harbu suke samun kulawa.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da lamarin, ta bayyana cewa an fara bincike a kan cutar Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 17 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta a garin Okpeilo-Otukpa, karamar hukumar Ogbadilo da ke jihar Benue.

Wata sanarwa da aka saki a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, daga kwamishinan lafiya na jihar, Dr Emmanuel Ikwulono, ya tabbatar da mace-macen, jaridar ThisDay ta ruwaito.

Ya kara da cewa sauran wadanda suka harbu da cutar na samun kulawar likitoci a asibitoci daban-daban.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati na sane da barkewar cutar sannan cewa ta kafa bincike domin gano musababbin cutar.

Ikulono ya kara da cewa Gwamna Samuel Ortom ya amince da kudade domin gudanar da binciken da ya kamata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here