Legas: Sojojin Najeriya Sunyi wa Gwamnan Tayin Dakaru
Gwamnan Jihar Legas ya ce rundunar sojojin Najeriya ta yi masa tayin ba shi taimakon dakaru domin daƙile zanga-zanga a jihar, a cewar rahoton Reuters.
An ruwaito Babjide Sanwo-Olu yana magana ne a hirarsa da wani gidan talabijin a yau Alhamis, yana mai cewa “shugaban sojoji ya kira ni ranar Laraba cewa idan ina buƙatar sojoji su zo za su fito kan tituna”.
Read Also:
Ya ce lamarin na kare lafiyar sana’o’i ne da kuma gine-ginen gwamnati, waɗanda wasu tsageru suka riƙa kai wa hari.
Ƙungiyoyin kare haƙƙi da kuma waɗanda suka shaida lamura da idanunsu sun ce sojoji sun buɗe wa masu zanga-zanga wuta ranar Talata. Amnesty International ta ce mutum 12 aka kashe a wuri biyu a Legas.
Sai dai rundunar sojojin ta musanta cewa dakarunta ne suka aikata harbe-harben.
Yanzu haka akwai dokar hana fita a birnin Legas ta awa 24 amma gwamnan ya ce akwai yiwuwar a sassauta ta ranar Juma’a idan abubuwa sun lafa.