LEGAS:Akalla an Samu Mutane 30 Daka Raunana a Lekki Toll Gate

ne sun buɗe wuta ga masu zanga-zangar #ENDSARS a Lekki Toll Gate da ke Legas a yammacin Talata.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa akwai marasa lafiya goma da ke babban asibitin jihar da kuma 11 da ke asibiti Reddington sai kuma guda huɗu da ke asibitin Vedic.

Gwamnatin ta ce akwai mutum biyu da ke ƙarkashin sashen kulawa na musamman sai kuma an sallami mutum uku.

Gwamnatin jihar ba ta tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba a wurin da lamarin ya faru, sai dai waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa akwai wasu da aka harbe suka mutu a wurin.

Lamarin dai ya faru ne a yammacin Talata a Lekki da ke Legas inda wasu da ake zargin jami’an tsaro ne suka buɗe wa masu zanga-zangar wuta, sa’o’i kaɗan bayan an saka dokar hana fita ta awa 24.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here