Likita ‘Daya ne ke Duba Marasa Lafiya 45,000 a Arewacin Najeriya – NMA
Kungiyar likitocin Najeriya – NMA ta ce a yanzu likitoci dubu 24 ne suka rage a kasar domin kula da lafiyar al’ummar kasar fiye da miliyan 200.
Shugaban NMA, Ojinmah Uche wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa karancin likitoci a kasar ya saba da irin shawarar da hukumar lafiya ta duniya – WHO ta bayar na adadin likitocin da za su iya duba marasa lafiya.
Read Also:
A cewarsa “A yanzu likita daya ne ke duba marasa lafiya 30,000 a kudancin Najeriya a yayin da likita daya ne ke duba marasa lafiya 45,000 a arewacin kasar.”
Ojinmah ya ce ficewar jami’an kiwon lafiya daga Najeriya zuwa kasashen waje babban lamari da ke bukatar hukumomi su sa’ido.
Bayanai sun ce a yanzu Najeriya ce kasa ta uku a yawan likitocin kasar waje da ke aiki a Birtaniya. Kasashen Indiya da Pakistan su ne kan gaba a yawan likitocin kasar waje a Birtaniya.