Likita ya Kamu da Cutar Korona Bayan ya yi Allurar Rigakafin Cutar
Tuni kasashen duniya, musamman a nahiyar Turai, suka fara amfani da allurar rigakafin cutar korona.
Jama’a da dama, musamman a nahiyar Afrika, na nuna shakku da alamun tambaya a kan allurar rigakafin.
Wani rahoton kafar yada labarai ta BBC ya bayyana yadda wani likita a kasar Amurka ya kamu da koron bayan an yi masara allurar rgakafi.
Wani likita da ke aiki a wani asibiti a Jihar California ta kasar Amurka ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan yi masa allurar rigakafi.
Read Also:
Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa an yi likitan allurar rigakafi ta kamfanin Pfizer a makon da ya gabata.
Sakamakon faruwar hakan, kamfanin Pfizer ya bayyana cewa cigaba da bibiyar dukkan wasu bayanai dangane da sabuwar allurar rigakafin.
“Rigakafin na bukatar lokaci kafin ta ginu a jikin mutum, mutum zai iya kamuwa da kwayar cutar kwanaki goma kafin ko bayan yi masa allurar rigakafin,” a cewar wata sanarwa da kamfanin ya fitar.
A ranar 18 ga watan Disamba ne likitan mai suna Matthew W., dan shekaru 45, ya sanar da cewa an yi masa allurar rigakafin korona ta kamfanin Pfizer.
A lokacin, Matthew ya bayyana cewa bayan ciwon wuni guda da hannunsa ya yi, allurar ba ta da wata illa.