Jam’iyyar Macron ta Rasa Kusan Kujeru 100 a Majalisar Dokokin Faransa
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya samu gagarumin koma-baya a siyasa, bayan da gwamnatinsa ta hadaka ta rasa rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Read Also:
Jam’iyyarsa ta hadakar ta rasa kusan kujeru 100 a majalisar, yayin da jam’iyyar Marine Le Pen ta masu tsatstsauran ra’ayin rikau da kuma jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayin kawo sauyi ta Jean-Luc Mélenchon suka samu kujeru da dama a majalisar.
Mr Melenchon ya kasance shi ne babban abokin hamayyar Mr Macron a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Afrilu, inda a yanzu kuma ya zamo jagoran ‘yan adawa.
Kasa da wata biyu kenan da Mr macron ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu.