Wani Magidanci Ya Gano Matarsa Tana Neman Maza

Wani mutum mai suna Mlekeleli Masondo ya bayyana yadda ya gano matarsa tana ha’intarsa.

A cewarsa, yayi amfani da sunan bogi, inda suka yi ta soyayya da matarsa a tunaninta wani ne daban.

Ya ce, ya bukaci ta hana mijinta hakkin aurensa, yadda zai kwashi gara idan sun hadu, kuma ta amince Wani mutum mai suna Mlekeleli Masondo, dan asalin South Africa, ya yi wata wallafa a shafinsa na Facebook, ta yadda yayi amfani da shafin bogi na kafar sada zumuntar zamani, har ya gano matarsa tana ha’intarsa.

Kamar yadda Masondo ya wallafa, ya yi amfani da sunan bogi, har matarsa ta amince da za su fita yawon shakatawa a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Ya ce ta dade tana hanasa hakkinsa na aure domin ta tattala wa saurayinta, ya kwashi gara a ranar farko da za su hadu.

Mutumin ya ba wa maza da dama dabarar gano idan matansu suna ha’intarsu. Masondo ya bayyana yadda suka yi ta sheke aya da matarsa a kafar sada zumunta amma bata san cewa shine ba.

Ya ce da zarar ya tafi aiki, sai matar ta tsunduma da soyayya da saurayin, a tunaninta wani ne ba shi ba, har tana tura masa kudi.

Kamar yadda ya wallafa, “Mata ta ta hadu da wani a Facebook, inda suka fara soyayya na tsawon sati 4.

Gayen baya aiki, da zarar na tafi aiki, sai su fara hirar soyayya, har kudi take tura masa.”

Ya bayyana yadda matarsa tayi masa karyar cewa tana bukatar kudi don ta tura wa kanwar mahaifiyarta da ke fama da ciwo, amma ta tura kudin ga saurayinta.

Ya ce ta bayyana wa saurayin cewa babu abinda ta nema ta rasa, kawai tana kwasar nishadi ne.
Ya ce saurayin ya bukaci ta hana mijinta hakkin aurensa, saboda ya samu ya kwashi gara ranar da za su hadu, kuma ta amince da hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here