Mahara Sun Kai Hari Makarantar Sakandire a Jihar Oyo

 

Oyo – Wasu mahara da ake kyautata zaton Makiyaya ne, ranar Alhamis, sun kai farmaki wata Makarantar Sakandiren gwamnati a jihar Oyo, sun jikkata ɗalibai da Malamai.

Vanguard ta gano cewa maharan makiyayan sun kutsa kai cikin makarantar Community Grammar School da ke garin Alaropo Nla a ƙaramar hukumar Oriire, jihar Oyo.

Wani ganau da ya shaida duk abinda ya faru ya ce, makiyayan da suka kai mutane sama da 20 sun shiga makarantar tare da dabbobinsu kana suka raunata wasu ɗalibai da malamai.

Wasu daga cikin Malamai da ɗalibai da lamarin ya shafa, cikinsu har da wani mai suna Mista Paul Olabode, makiyayan sun yanke su da wuƙake da Adduna, wssu kuma sun karye a kafafu da hannu.

Ƙarin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com