Majalisar Dattijan Najeriya ta Dakatar da Sanata Abdul Ningi

 

Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya, Sanata Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun ‘zubar da ƙimar majalisar.’

A wani zama mai cike da hatsaniya, majalisar ta bai wa sanatocin damar yin bayani ɗaya bayan ɗaya, inda kusan dukkanin su suka nuna rashin jin daɗi kan kalaman sanata Ningi a wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC.

Me sanata Ningi ya shaida wa BBC?

Tattaunawar da Sanatan yayi a filin Gane Mini Hanya da sashen Hausa na BBC ke watsawa a rediyo duk ranar Asabar, ita ce ta tayar da ƙura a faɗin ƙasar, bayan da ya furta cewa akwai kasafin kuɗin ƙasar kala biyu da ake da su a yanzu haka.

Ya ce “Bajet (budget) ɗin da aka yi, bayan wanda majalisa ta yi a fili an koma an yi wani bajet a ƙarƙashin ƙasa,”

Ya ƙara da cewa “abubuwan da muka gani sabbi ba mu taɓa jin labarinsu ba, amma har yanzu ƙwararru na fannin kuɗi da muka ɗauka suna kawo mana bayanan yadda abubuwan suke faruwa,”

“Misali, an yi bajet na tiriliyan 28 amma mu da muka kididdige sai muka ga bajet ɗinnan kusan tiriliyan 25 ne, ka ga akwai tiriliyan uku, a ina suke?”

Sanata Ningi ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan lamarin kuma idan suka kamalla za su kai har wurin shugaban ƙasa domin tambayar sa ko yana da masaniya kan abun.

Matsayar majalisa kan sanata Ningi

A lokacin zaman majalisar na yau Talata, sanata Adeola Solomon da ke wakiltar yankin yammacin jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya ne ya mika bukatar tattauna batun zarge-zargen a zauren majalisar, inda kuma sanata Ned Nwokor daga Edo ta Kudu ya mara wa bukatar baya.

Bayan wasu sanatocin sun fara tattaunawa, an bai wa Sanata Abdul Ningi damar yin nasa bayanin, inda ya bayyana cewa bayanin da ake yaɗawa “ya sha bamban da abin da ya faɗa a cikin tattaunawarsa da BBC.”

Bayan kwashe dogon lokaci sanatoci na ta sabata-juyata, sai sanata Jimoh Ibrahim da ke wakiltar kudancin Ondo, ya ce ya kamata a dakatar da sanata Ningi har tsawon watanni 12 tare da datse duk wasu abubuwan da yake samu.

To sai dai kuma sanata Asuquo Ekpenyong daga jihar Cross River ya nemi da a mayar da dakatawar watanni shida.

Amma daga bisani, sanata Garba Maidoki daga jihar Kebbi ya buƙaci a rage hukuncin zuwa dakatarwa na wata uku, tare da bai wa Ningi damar rubuta takardar neman afuwa.

A ƙarshe majalisar ta cimma matsaya, inda ta yanke wa sanata Ningi dakatarwa ta tsawon wata uku.

Martanin kungiyar sanatocin arewa

Wata takarda mai dauke da sa-hannun sanata Abdul Ningi wanda shi ne shugaban kungiyar sanatocin arewacin Najeriya ta ‘Northern Senators Forum’, ta nuna yadda sanata Ningi ya yi murabus daga shugabancin kungiyar.

“Na ajiye aikin shugabancin kungiyar sakamakon abubuwan da suka biyo bayan takaddamar da ta wakana a zauren majalisar dattawa.”

Yanzu haka dai mataimakin sanata Abdul Ningi a kungiyar ne wanda ba a fayyace kowane ne ba shi ne zai jagoranci kungiyar.

Kalaman na sanata Ningi dai da ya yi a BBC Hausa da ma ba su yi wa fadar shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu daɗi ba, inda mai magana da yawunsa ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya musanta kalaman sanatan.

Haka nan lamarin ya janyo cece-ku-ce a faɗin ƙasar, saboda ana ganin hakan a matsayin wata fallasa ta badaƙala da ke gudana a ƙarƙashin ƙasa.

Me dakatarwa daga majalisa ke nufi?

Dakatar da dan majalisa walau dai na dattawa ko kuma na wakilai na nufin dakatar da dukkan wasu damarmaki da dan majalisar yake da su.

Sanata Shehu Sani wanda tsohon dan majalisar dattawa ne daga jihar Kaduna, a shafinsa na X, ya wallafa ma’anar dakatar da dan majalisa kamar haka:

“Hakan na nufin sanatan ba zai rinka halartar zaman majalisar da na kwamitoci ba har tsawon lokacin da aka deba masa na dakatarwar. Ba za a bar shi ya je ofis ba har ma farfajiyar majalisar ba zai leka ba.

Sannan kuma ba zai rinka daukar albashi da alawus-alawus ba.” In ji tsohon dan majalisar.

Dangane kuma da martaninsa ga dakatarwar, sanata Shehu Sani wanda shi ma ya taba fuskantar irin wannan kalaubale amma ba a dakatar da shi ba ya ce:

“Lokacin da na fito fili na bayyana yawan kudin gudanarwar ‘yan majalisa, shugaban majalisar dattawan lokacin ne ya kare ni daga dakatarwa. Idan mutum ya cika surutu, jiknasa ne zai fada masa. Shi ya sa ma ko da ‘yan majalisa masu hamayya ba sa hamayyar sosai.” In ji Sanata Shehu Sani.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here