ɓatan Kuɗin Man Fetur: Majalisar Wakilai ta Gayyaci Ministar Kuɗi
Kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke bincike kan zargin ɓatan kuɗin man fetur ya gayyaci ministar kudin ƙasar Zainab Shamsuna Ahmed, da Sakataren gwamnatin tarraya Boss Mustapha, da kuma ministan shari’a Abubakar Malami.
Yana neman su bayyana gabansa a wani ɓangare na binciken da yake yi.
Shugaban kwamitin, Mark Tersee Gbillah ne ya bayar da umarnin gayyatar jami’an gwamnatin, bayan kwamitin ya koma sauraron bahasi kan zargin ɓacewar kuɗin gangar man fetur miliyan 48 da aka sayar wa China da wasu masu kwarmata bayanai suka bayyana.
Read Also:
Kwamitin na bincike ne kan zargin ɓatan sama da dala biliyan 2.4 na man fetur da aka fitar ba bisa ƙa’ida ba, domin sayar da shi, tun daga shekarar 2014 zuwa yau.
Mista Gbillah ya ce kwamitin ya ba da umarnin ne domin sanin irin rawar da – ma’aikatar kuɗi da sauran hukumomin gwamnati – suka taka musamman kan abin da ya shafi tsarin masu kwarmata bayanai.
”Mafi yawan matsalolin – abin da ya kamata mu bincika game da tsarin masu kwarmata bayanai – na tasowa ne tsakanin ma’aikatar kuɗi da ofishin ministan shari’a”.
Tun da farko kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila wanda ya samu wakilcin Isiaka Ibrahim Ayokunle, ya nuna damuwa game da raguwar kuɗin shiga da ƙasar ke samu daga sayar da ɗanyen man fetur.
Ya ce abu ne mai tayar da hankali zargin da masu kwarmata bayanan suka yi cewa fiye da dala biliyan 2.4 na kuɗin gangar mai miliyan 48 ne suka ɓace a ƙasar.