Atiku ya Gaza Cika Sharuɗɗan Cin Zaɓe – INEC

 

Hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta ce ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gaza cika sharuɗɗan da tsarin mulkin ƙasar ya gindaya kafin a ayyana shi matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

INEC ta bayyana haka ne a matsayin martani kan ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar ya shigar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Ta dai buƙaci kotun ta yi watsi da ƙorafin da ɗan takarar ya shigar gabanta yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.

Hukumar ta ce Atiku ya gaza samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a aƙalla kashi biyu cikin uku na jihohin ƙasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja, wanda hakan na cikin sharuɗɗan cin zaɓe a ƙasar.

Game da ƙorafin saɓa dokar zaɓe, INEC ta ce an gudanar da zaɓen ne bisa dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ba tare da almundahana ba, kamar yadda masu ƙorafin suke zargi.

Hukumar zaɓen ta sake jaddada cewa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC shi ne halastaccen zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

Game da ƙorafin rashin samun rinjayen ƙuri’u a Abuja da ake yi wa Tinubu, INEC ta ce kundin mulkin Najeriya bai fitar da wani matsayi na musamman a kan ƙuri’un babban birnin ƙasar ba.

Domin haka, a cewarta ƙuri’un Abuja daidai suke da ƙuri’un kowacce jiha ta fuskar matsayi.

Atiku Abubakar tare da jam’iyyarsa ta PDP sun garzaya kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe ne domin ƙalubalantar sakamakon da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here