Majalisar Dokokin Amurka ta Bai wa Gwamnatin ƙasar Damar ƙara Yawan Bashin da ya Kamata ta Ciwo
‘Yan majalisar dokokin Amurka ta bai wa gwamnatin kasar dama ta dan lokaci domin ƙara yawan bashin da a ƙa’ida ya kamata ta ciwo, wanda ƙwararru ke cewa yin hakan ya kawar da wata gagarumar matsala ta tattalin arziki d aƙasar ba ta taba shiga a tarihi ba.
Read Also:
Dukkan ‘yan jam’iyyar Democrats 50 suka kaɗa ƙuri’ar amincewa, yayin da 40 na jam’iyyar Republican suka ƙi amincewa, sai kuma biyu da ba su kada ƙuri’ar ba.
Wakiliyar BBC ta ce dole sai ‘yan majalisar wakilai sun amince da dokar kafin Shugaba Joe Biden ya rattaba ma a hannu.
Dokar da zai sanyawa hannu za ta kara adadin kudin da za a ciwo bashi da dala biliyan 480, domin cike giɓin kudaden da za a kashe zuwa 3 ga watan Disamba mai zuwa.