Shirin Dawo da Rundunar SARS: Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta Musanta Rahotan

 

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta musanta wasu rahotanni da ake yadawa a kafafe daban-daban cewa, shugaban rundunar Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin sake kafa rundunar musamman ta yaƙi da ƴan fashi da makami da ake kira SARS, wadda aka rushe.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ko alama ba ta da wata niyya ta dawo da rundunar, wadda ta riga ta rushe ta, ta kowa ce siga.

Sanarwar ta ce tuni Sufeto Janar na ƴan sanda ya sake fasalin aikin rundunar kasar, ta yadda aka maye gurbin da aka samu na rashin waccan rundunar ta musamman ta SARS.

A sanarwar ta ce, yanzu ba abin da shugabancin ƴan sandan na ƙasa ya mayar da hankali fa ce yadda zai ɓullo da sauye-sauye da za su sa ya bar tarihin rundunar da za ta kasance mai aiki tukuru, da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukanta da mutunta jama’a da bin doka.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here