Majalisar Dattawa na Barazanar Bayar da Umarnin Damko Shugaban NDLEA da NSA
Majalisar dattawa na barazanar bayar da umarnin damko shugaban NDLEA, Buba Marwa da NSA Babagana Monguno.
Majalisar ta ce ta tura wa ofishin NSA da hukumar NDLEA gayyata amma har yanzu shiru ka ke ji babu labari
Majalisar na zargin NDLEA da yin sama da fadi da wasu kudi har N467 miliyan, sai ofishin NSA da ake zargi da lamushe N3.5 biliyan.
FCT, Abuja – Majalisar dattawan Najeriya ta yi barazanar bayar da umarnin damko shugaban hukumar NDLEA, Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya da kuma mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno, kan kin amsa gayyatarsu da suka yi.
Daily Trust ta wallafa cewa, Ofishin odita janar na tarayya ya mika tuhuma kan NDLEA da ofishin NSA a wani rahoto na 2016, wanda kwamitin majalisar kan asusun gwamnati ya duba.
An mika tuhuma 11 ga NDLEA kan lamurra da suka hada da watanda da kudade da za su kai miliyan N467, Daily Trust ta rawaito.
Read Also:
Rahoton kudin ya zargi cewa an aikata almundahanar ne a shekarar 2015 kafin a nada Marwa a matsayin shugaban hukumar.
Ofishin NSA Monguno kuwa, ana zarginsu da waskar da kudi da suka kai N3.5 biliyan da aka ware na siya ababen hawan hafsoshin sojoji.
Sanata Mathew Urhoghide, wanda ke shugabantar kwamitin majalisar wurin bincikar zargin, ya ce jami’ai daga dukkan hukumomin ba su amsa gayyatar da aka mika musu ba domin su yi bayani kan zarginsu.
Urhoghide ya sha alwashin cewa majalisar dattawan za ta yi amfani da karfin ikon da kundun tsarin mulki ya bata wurin tirsasa Marwa da Monguno su bayyana a gaban kwamitin.
“Ba mu duba girman mutum domin babu wanda ya gagare mu. Muna shawartarsu da su bayyana a gabanmu. Muna jan kunnensu a karo na karshe, za mu yi amfani da karfin ikon da kundun tsarin mulki ya ba mu wurin tirsasa su domin bayyana a gabanmu,”
yace.
A bangaren ofishin NSA, ya ce “NSA ya zo da kan shi domin karin bayani. Ba mu da wata matsala kai tsaye da shi. Mun bukaci ya turo wani ko kuma ya zo da kan shi.”
NDLEA ta ce ba ta san da labarin gayyatar ta da aka yi ba daga majalisar dattawan.