Manoman Sokoto Sun Koka da Rashin Tsaro

Mazauna Gudu da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto, sun koka a kan rashin tsaro.

Sun ce ‘yan bindiga sun addabesu, har ta kai ga basu iya kwana a gidajensu saboda bala’i.

Sun ce suna tserewa kasar Nijar, su koma gidajensu washegari don gudun a yi garkuwa dasu.

Mazauna kananun hukumomin Gudu da Tangaza da ke jihar Sokoto, sun koka a kan yadda al’amuran ‘yan bindiga suka takura su har suke kai ga neman wurin rabewa a kasar Jihar.

A cewarsu, ‘yan bindiga suna zuwa garuruwansu da yamma, su amshe dukiyoyi masu tarin yawa daga hannayen masu hali a cikinsu, ko kuma su yi garkuwa da su.

Daya daga cikin mazauna kauyen Kurdula, ya bayyana wa BBC cewa da yawansu suna tserewa kasar Nijar da yamma sai su koma gidajensu da safe.

Kamar yadda ya bukaci a boye sunansa, yace “Al’amarin ya kazanta a kananun hukumomin Gudu da Tangaza.

“Duk dare, ‘yan bindiga suna zuwa kauyakunmu da bindigogi, sai su yi ta zagayen gidaje. Idan ka nuna musu baka da kudi, sai su tilasta maka nuna musu gidan mai kudi don su yi garkuwa da shi.

“Ko a ranar Lahadi, sun yi garkuwa da mutane 2, kuma har yanzu basu sako su ba, saboda basu riga sun biya su kudaden fansa ba.”

Kwamishinan tsaro na jihar, Garba Moi Isa, ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin jihar tana samun nasarori wurin yaki da ta’addanci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here