Kotu ta Yanke wa Wani Mutum Zaman Gidan Yari na Tsawon Shekaru Biyar

 

Wani mutumi dan kasar Faransa zai sha daurin shekaru biyar a gidan maza.

Kotun kasar ta yanke masa wannan hukunci kan harbe wani zakara da yayi saboda kawai ya dame shi da cara.

Mai zakaran ne ya shigar da karar inda ya nemi a bi ma dabban nasa hakkinsa.

Rahotanni sun kawo cewa an zartar da hukuncin daurin shekaru biyar a kan wani mutumin kasar Faransa sakamakon kama shi da laifin bindige wani zakara tare da tsire shi da karfe saboda ya dame shi da cara.

Makwabcin zakaran wanda aka ambata da suna Marcel wanda ya fito daga jihar Ardèche, ne ya harbe shi a watan Mayu bayan carar da yake yi ya fusata shi.

Mammalakin zakaran, Sebastien Verney, shine ya rubuta wata takarda don neman a bi wa zakaransa hakki.

Kuma tuni akalla mutane dubu dari daya suka rattaba hannu a kan takardar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

An kuma kama makwabcin nasa da aikata laifin yi wa dabba mugunta da sauran laifuka.

Baya ga hukuncin dauri da aka yanke masa, an kuma ci tararshi kudi €300 tare da dakatar da shi daga rike duk wani maƙami tsawon shekara uku.

A cewar mai zakaran, Mista Verney: “Wannan ba zai taɓa gyara abin da ya aikata ba.”

A takardar karar da ya rubuta, ya yi magana kan “mummunan abin bakin ciki” da ya fada wa iyalan, yayin da ya yi kira a kan cewa kada kauyuka su zama wurin ajiyar kayan tarihi.

“Su waye za su sake fadawa cikin wannan barazana? Tattabarun da ke kuka, girbin alkama, noman tumatir, kukan jaki, kararkƙararrawar agogo ko kuma kiwon shanu?”

Wannan ita ce takaddamar da ta shafi zakara da ta mamaye kafafen yada labarai a baya-bayan nan a kasar Faransa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here