Gwamnatin Masar ta Dage Dokar Ta-baci Bayan Shekaru 4
Shugaban kasar Masar Abdel Fatah al Sisi, ya cire dokar ta-bacin da aka sanya a kasar tun a watan Afrilun 2017.
Read Also:
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mr al Sisi ya ce ba zai kara wa’adin dokar ba saboda kasar a yanzu ta zama dausayin zaman lafiya da tsaro.
Dokar ta bacin wadda aka sanya ta bayan harin da aka kai wa wasu majami’u biyu, ta kara wa yan sanda karfin iko da kuma ragewa fararen hula ‘yanci.
Haka kuma ta ba da damar a rika yanke wa fararen hula hukunci a gaban kotunan sojoji.