Masar: Cin Zarafi ya sa Mata Sun Zama Jarumai a Kasar

Ga mata da ‘yan mata a Masar, cin zarafi ya daɗe yana faruwa, amma waɗanda abin ya shafa yanzu suna gwagwarmaya ba kamar da ba, in ji Salma El-Wardany.

Duk matar da na sani a Masar tana da labarin cin zarafin mata, cin zarafi ko fyaɗe.

Ya zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullun a wannan ƙasa, inda mata suke ɗaukar kayan ado ba su da muhimmanci game da salon, kuma game da kariya.

Tsawon shekaru, al’adun gargajiya, da addini da kuma ra’ayin mazan jiya na sanya mata yawan yin shiru lokacin da ake lalata da su saboda zargin waɗanda ake zalunta ya zama ruwan dare.

Amma yanzu, mata da ‘yan mata a ƙarshe sun daina yin shirun da suka shafe shekara da shekaru suna yi.

Suna zuwa kafofin watsa labarai don ba da labarinsu na cin zarafi don ƙarfafa juna da kira ga yin adalci.

An fara ne a watan Yuli, lokacin da mata da dama suka yi zargin cewa wani matashi mai suna Ahmed Bassam Zaki ɗan shekaru 22, ya ci zarafinsu.

Jim kaɗan bayan kama shi, an fara tuhumarsa da cin zarafin wasu mata uku, dukkaninsu ‘yan ƙasa da shekara uku, sannan ya riƙa yi wa mace ta huɗu barazana, amma ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Me ya sa aka daure ‘yar uwata saboda rawa a TikTok?’

Nadeen ta ce ta cika da farin ciki sakamakon yadda mutane da dama suka taso dangane da wannan al’amari, ta ce “a cikin ‘yan makonni akwai wata sabuwar doka da aka ɓullo da ita a majalisar dokokin ƙasar don kare mata daga fuskantar cin zarafi.

Fyaɗen da aka yi wa wata ‘yar fafutuka Sabah Khodir ta jefa mutane cikin damuwa, sai da lamarin ya sa ta fice daga ƙasar ta koma Amurka a bara.

Duk da haka, Sabah na taimaka wa mata tare da ba su shawarar tuntuɓar lauyoyi da masu ba da magani, kuma yanzu tana ganin an ba da ladan ƙoƙarinta.

A farkon wannan shekarar ne babbar hukumar kula da harkokin addini ta Masar ta fitar da sanarwa don nuna goyon baya ga mata, inda ta bayyana cewa tufafin mace ba hujja ba ce ga cin zarafi.

Sannan hukumar ta kuma nemi yawancin masallatai su yi huduba dangane da kyamatar cin zarafin mata da ake yawan samu a kasar.

Kiran hukumar ya kawo karshen zargin da wasu ke yi na cewa shugabannin addinai ba sa cewa komai dangane da batun.

Taurari da fitattun mutane duk sun fito don yin Allah wadai da ƙaruwar cin zarafin mata da ake samu.

Omar Samra, wani dan rajin kare hakkin dan adam na daga cikin wadanda suka yi magana a shafukan sada zumunta.

“Na yi matukar fusata da taƙaici game da abin da ke faruwa, ba na tunanin za a taɓa yin daidai har sai maza sun dauki alhakin abin da suka aikata.”

Masu rajin kare haƙƙin mata a ƙasar sun kwashe shekara da shekaru suna neman a samar da ingantaccen tsarin doka game da laifukan lalata, sai dai har yanzu, ba a cimma wata nasara ba.

Rothna Begum, mai bincike kan hakkin mata a ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Human Rights Watch, ta ce duk da cewa gwamnati na nuna tana goyon bayan mata, amma akwai koma baya ga mata a ɓangaren jama’a, gami da yanar gizo.

“Mahukunta sun zarce iyaka wajen kamo matan da suka shahara a shafukan sada zumunta da ke sanya bidiyoyinsu a TikTok,” in ji ta.

Har ila yau rahoton cin zarafin da aka samu a wani otal da ke birnin Alƙahira a shekarar 2014 ya sake tayar da hankali kwarai da aniya.

Lamarin ya haɗar da wasu mutane tara, da suka fito daga wata zuri’ar masu ƙarfin faɗa a ji da ke Masar, kuma ana zarginsu ne da cin zarafin wata ƙaramar yarinya tare da ɗaukar bidiyon ta’asar da suka tafka tare da yaɗawa tsakanin abokansu.

Yayin da mai gabatar da kara na gwamnati ya ba da umarnin kame mutanen da ake zargi, sun kuma samu wasu shaidu da ke da alaka da shari’ar.

A cewar Rothna Begum, gwamnati na barin mata da tunanin cewa ”idan ka kai rahoton fyade ko kuma ka zama sheda, kana iya samun kan ka a cikin hadari”.

Mata na cikin tsaka mai wuya a Masar kwarai da gaske, abin da ke karawa fafutukar kare su armashi a halin da ake ciki.

Duk da cewa tsarin dokar da ake da shi bai basu wata cikakkiyar kariya ba, matan Masar sun fito da kwarin guiwar su suna tonon sililin abin da ke faruwa domin dunita ta ji.

Mona Eltahawy wata ‘yar kasar Amurka kuma mai fafutuka ta ce “tana da kwarin gwiwa… cewa juyin juya halin mata ya fara”, duk da shaidar da ke nuna cewa hukumomi na kokarin yin shiru da danniyar da ake yi wa mata a duk fadin kasar ta hanyar kama wadanda ke wallafa bidiyonsu a TikTok.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here