2023: Masu sa ido Kan Zaɓe Daga ƙasashen Renon Ingila Sun iso Najeriya
Masu sa ido a zaɓe daga ƙasashen renon ingila sun iso Abuja, babban birnin Najeriya, gabanin babban zaɓen ƙasar na shugaban ƙasa da kuma ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar.
Kungiyar ta kunshi mutum 16 da suka fito daga ƙasashen renon ingila wanda ya kunshi ‘yan siyasa da jami’an diflomasiyya da masana bangaren shari’a da masu kare hakkin ɗan adam da kuma daidaiton jinsi.
Read Also:
Da yake jawabi ga manema labarai a yau Litinin, shugaban kungiyar wada kuma shi ne tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki, ya ce kudurinsu shi ne sa ido da kuma duba shirin da aka yi kafin zaɓe da ayyukan ranar zaɓe da kuma bayan zaɓe.
Mista Mbeki ya lura da cewa zaɓukan Najeriya za su kasance manya a nahiyar Afirka kuma sakamakonta na da matukar muhimmanci ga ɗaukacin nahiyar.
A don haka ya buƙaci jam’iyyun siyasa a ƙasar da ‘yan takara da kuma magoya bayansu da su tabbatar da ganin an yi zaɓukan ranar 25 ga watan Febrairu cikin koshin lafiya da kuma gaskiya.
An kiyasta cewa mutum miliyan 93.4 ne suka yi rajista domin samun damar kaɗa kuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya a cikin rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin Najeriya.