Malamin jinya ya Shiga Hannu Kan Zargin yi wa Marasa Lafiya fyaɗe

 

‘Yan sandan Uganda sun kama wani malamin jinya kan zargin yunkurin yi wa wasu mata masu ciki biyu fyaɗe a wani asibitin gwamnati mai suna Entebbe da ke da nisan kilomita 40 da Kampala, babban birnin ƙasar.

Mataimakin mai magana da yawun ‘yan sandan birnin, Luke Owoyesigire, ya ce an kama wanda ake zargin ne mai suna Kutesa Denis a jiya Lahadi kuma yana tsare a ofishin ‘yan sanda da ke Entebbe.

Ana zargin cewa sai da Kutesa ya bai wa matan biyu da ke sashin kula da mata na asibitin wani kwayar magani suka sha kafin ya ci zarafinsu.

An kuma gano wasu kwayoyi a gidansa bayan gudanar da bincike da kuma wata takarda da ake zargin ya rubuta inda yake rokon a yi masa addu’a kan abin da yake fuskanta mara kyau a yawan lokuta.

‘Yan sanda sun ce akwai yiwuwar ƙarin wasu da aka ci wa zarafi, inda suke buƙatar mutane su fito su yi magana.

Darektan asibitin, Dakta Peterson Kyebambe ya faɗa wa BBC cewa lamarin ya sanya yanzu sun fara saka ido kan likitoci da ma’aikata ko kuma kafa kyamarorin tsaro a faɗin asibitin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here