Ana Abu a Duniya: Matasa Sun Cinnawa Coci Wuta Akan Satar Mazakuta

Ƴan Sanda sun cafke wasu matasa da ake zargi da ɓarnata kayan al’umma saboda ƙona coci.

Matasan na garin Daudu sun cinna wa wani coci wuta ne kan iƙirarin cewa faston cocin yana satar mazakuta – Matasan sunyi iƙirarin cewa faston yana haɗa baki da wani mutum ne don sace mazakutar matasa a garin.

Fusatattun matasa a garin Daudu a ƙaramar hukumar Gina, a ranar Talata, sun ƙona Divine Shadow Church kan alaƙanta mai cocin da satar mazakuta a garin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwana ki uku da suka shuɗe, matasan sun yi zanga zanga a babban titin Makurdi – Lafia kan abinda suka kira ‘batar mazakutar’ mutum shida cikin wata guda a garin.

Matasan da suka ƙona cocin sun yi ikirarin cewa mai cocin, Manzo Uhembe da wani da suka haɗa baki, Noah Saka ne masu kitsa yadda ake satar mazakutar.

Nongu Francis, wani da ya yi iƙirarin cewa wani mutum daban da ya kashe kansa ya sace masa mazakuta a ranar 10 ga watan Oktoba.

Francis ya ce marigayin ya kai shi gonarsa don yin wani wanka na musamman kuma tun bayan lokacin baya ya iya saduwa da mace.

Ya ce abinda ya faru da shi ya faru da wasu da dama da ke zargin marigayin ne ya musu tsafi kuma daga baya sai ya tura su wurin Manzo don ya musu aikin dawo da mazakutar su.

Francis ya ce ba bata mazakutarsa ta yi ba sai dai baya iya saduwa kuma a yanzu bai san yadda zai yi tunda mutumin ya mutu.

Wani matashi da ya ce sunansa Jonah ya ce yawan ɓatar mazakuta a unguwar ne ya janyo ƙona cocin mallakar faston da ake zargi yana da hannu a lamarin.

“Munyi mamakin ganin mutumin da ke kiran kansa fasto zai rika satar mazakuta don yin tsafi. “Matasan sun ƙona cocinsa ne don ya zama darasi ga wasu masu irin wannan halin.

“Munyi imanin cewa idan ba a taka masa birki ba zai cigaba da wannan mummunar abin har ga mata,” inji wani matashin.

Anyi ƙoƙarin ji ta bakin faston amma hakan ya ci tura. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene ya tabbatar da ƙona cocin ya kuma ce an kama wasu kan zargin ɓannatar da kaya.

Ya ce ba dai-dai bane lalata kayan wanda ka ke zargi da wani abu. “Yayin da suke asibiti don tabbatar da zargin da suka masa, za mu ɗauki masu zanga-zangar a matsayin maɓarbata.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here