Ogun: Jami’an Tsaro Sun Damke Matashin da ya Hallaka Budurwarsa 

Ana zargin wani Matashi da laifin kashe Budurwa a dakin otel a jihar Ogun.

Wannan mutumi da ake zargi ya ce ya na cikin dukan Budurwar sai ta mutu – Daga nan ya sadada ya bar gawar ta, sai daga baya ma’aikatan otel su ka lura.

Vanguard ta fitar da rahoto cewa jami’an ‘yan sanda sun cafke wani mutumi mai shekara 31 da laifin yi wa buduwarsa mai shekara 26 kisan gilla.

Dakarun ‘yan sandan na jihar Ogun sun kama wannan Bawan Allah, Rexlawson Jonson, a dalilin zarginsa da ake yi da kashe sahibarsa a dakin otel.

Wannan mutumi da ake zargi da kisan-kai ya fito ne daga Ebonyi. Jaridar ta ce ya shiga hannun hukuma a ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, 2020.

Kakakin ‘yan sandan jihar Ebonyi, DSP Abimbola Oyeyemi, ya fitar da jawabi, ya ce rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar yin ram da Rexlawson Johnson.

‘Yan sanda sun cafko Rexlawson Jonson bayan Manajan wani otel da ake kira ‘Molayo Hotel’ mai suna Adebayo Aladesuyi ya kai kara gaban jami’ai.

Mista Aladesuyi ya shaida wa jami’an tsaro cewa yayin da su ke zagayen dakunan otel ne su ka ga gawar wata Budurwa da aka yi wa rauni a wuya.

“A dalilin karar da aka kawo, DPO na yankin Ibafo, Csp Jide Joshua ya jagoranci tawagarsa inda su ka kai gawar zuwa dakin ajiye gawa domin ayi bincike.”

Da aka yi bincike sai aka gano cewa marigayiyar ta shigo otel ne tare da wani mutumi wanda ake zargin ya tsere bayan ya yi nasarar aikata zuwa barzahu.

Kwamishinan ‘yan sanda na Ogun, CP Edward Awolowo Ajogun, ya ce sun kamo wannan mutumi, kuma ya bada labarin yadda ya kashe ta duka.

Johnson ya ce sun sabani da marigayiyar har ya kai ga duka, ya ce ya na cikin dukanta, ta mutu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here