Matsalar Tsaro na Barazana ga Aiwatar da Babban Zaɓen 2023 – HRW

 

Ƙungiyar da ke hanƙoron tabbatar da ƴancin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce rashin hukunta waɗanda aka kama da laifi a zaɓukan ƙasar na baya da kuma gazawar gwamnati na magance matsalar tsaro na barazana ga aiwatar da babban zaɓen ƙasar na 2023.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne al’ummar Najeriya za su zaɓi sabon shugaban ƙasa domin maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa’adin shugabancinsa, tare da na ‘yan majalisar dokokin tarayya, bayan mako biyu kuma za su fita domin kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi.

An dai yi ta samun barazanar tsaro game da zaɓen daga ƙungiyoyi daban-daban a faɗin ƙasar, ciki har da ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma da kudu maso gabashin ƙasar, waɗanda ke yunƙurin daƙile yiyuwar zaɓen.

Tarihin zaɓukan Najeriya ya nuna yadda zaɓukan ke cike da rigingimu da sauran laifukan zaɓe.

Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta ce zaɓen Najeriya na 2015 wanda ya bai wa shugaba mai ci Muhammadu Buhari nasara a matsayin ɗan takarar jam’iyyar adawa na farko da ya yi nasara zaɓen ƙasar shi ne ake gani wanda aka yi cikin kwanciyar hankali.

To amma an samu ‘yar hatsaniya a zaɓen 2019, ciki har da amfani da jami’an tsaro wajen yin barazana ga masu kaɗa ƙuri’a da kuma ‘yan dabar siyasa da ke yi wa ‘yan siyasa aiki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here