Dokar IPOB: An Mayar da Asabar Ranar Zuwa Makaranta a Madadin Litinin a Anambra
Hukumomi a jahar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya sun mayar da Asabar ranar zuwa makaranta a madadin Litinin, wacce ƴan awaren IPOB suka ayyana a matsayin ranar da babu aiki.
Wata sanarwa da gwamnatin jahar ta fitar ta ce an ɗauki matakin ne don bai wa ɗalibai damar yin karatu ba tare da wata matsala ba.
Mambobin IPOB sun ayyana Litinin a matsayin ranar kulle tare da tsaurara matakan taƙaita zirga-zirga a faɗin jahar.
Ƙungiyar na ƙara samun ƙarfi a yankin duk da haramtata da gwamnatin Najeriya ta yi.
Wannan ne karo na farko da wata gwamnatin jaha ta miƙa wuya ga barazanar ƙungiyar ƴan awaren.
Read Also:
IPOB na ci gaba da yin barazana sosai ga mutanen da suka ƙi bin umarninta na zama a gida.
A watan Nuwamba ne za a yi zaɓen gwamna a jahar Anambra.
Masu sa ido kan al’amuran siyasa sun ce miƙa wuya ga muradun IPOB zai ƙara mata azama tare da jefa yankin cikin rikici.
A watannin baya-bayan nan ƙungiyar ƴan awaren ta fafata da jami’an tsaro.
An kashe jami’an ƴan sanda da fararen hula da dama.
An samu ƙaruwar rikice-rikice a yankin kudu maso gabas inda ake kai hare-hare kan ofisoshin ƴan sanda da sauran wurare, kuma ana zargin ƴan tawayen ne da hakan.
Gwamnati na zargin jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu da rura wutar rikicin.
A yanzu haka yana fuskantar tuhuma kan ta’addanci da cin amanar ƙasa.