Mbaka ga Shugaban Kasa: Ka Bai Wa ‘Yan Najeriya Hakuri a Kan Mulkin Kama Karya
Babban faston nan na Enugu, Fr. Mbaka, ya ce zanga-zangar EndSARS ba don ‘yan sanda matasa suka yi ba kawai.
A cewarsa, mulkin kama karya da matasa suka gani, shiyasa suka fara zanga-zangar, ya san yanzu shugabanni za su fara kai masa hari .
Ya kara da cewa, an hana matasa abinci, aikin yi, asibitoci da tituna masu kyau, daga fitowa nuna rashin jindadinsu an fara kashesu Babban faston nan da ke jihar Enugu, Mbaka, ya ce zanga-zangar EndSARS ba don zaluncin ‘yan sanda aka yi ta ba, an yi ta ne saboda mulkin kama-karya, The Cable ta wallafa.
Ya fadi hakan ne a majami’a a ranar Lahadi, inda yace ya kamata shugaban kasa ya roki ‘yan Najeriya gafarar zaluncin da shugabannin da suka gabata suka yi da kuma nasa kura-kuren.
Faston yana daya daga cikin fastocin da suka taka rawar gani a lokacin kamfen din shugaban kasa a 2015.
A wata takarda da ya rubuta ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce Buhari ne zai ceci Najeriya da ‘yan Najeriya daga halin kangin rayuwa idan har suka zabeshi.
Read Also:
Bayan zaben shugaban kasan, Mbaka ya yi wani jawabi a Abuja, inda ya kambama Buhari har yake kiransa da “mutum mai kwarin guiwa”.
A wani jawabi da ya sake yi, Mbaka ya ce shugaban kasa ya zagaye kansa da miyagun mutane. “Buhari, da yakamata ya zama mafita ga mutane, yayi nasarar zagaye kansa da miyagun mutane wadanda basa fadi masa gaskiya,” a cewarsa.
A wannan jawabin nasa yace, “Wannan zanga-zangar ba ta EndSARS bace. Babu mai fada da gwamnati, sai dai fada da mulkin kama-karya.
“Kasar nan ba za ta taba gyaruwa ba. Kuna tunanin matasa za su cigaba da kallon shugabanni suna yin yadda sukaga dama? “Wasu daga cikin matasan da ke girma, sun fara yi wa miyagun shugabanni aiki, tun basu kai haka ba.
“Na san da zarar wasu daga cikin shugabannin nan suka ji wannan sakon nawa, za su fara kawo wa Fr. Mbaka hari. Amma ba damuwa ta bace, tasu ce. Watarana ba za su yi ba. “Mutanen da kuka hana ayyukan yi, abinci, tsaro, gidaje, wuta sannan ba su da asibitoci da tituna masu kyau, duk suka jure na wani lokaci.
“Don kawai rana daya sun nuna muku ba su ji dadi ba sai ku fara kashe su. Bayan kun kashesu ku dauki gawawwakinsu ku watsa a rafi? Babu ranar da Najeriya za ta gyaru.”