Borno: Dakarun Sojoji Sun halaka Wasu ‘Yan Boko Haram, Sun Rasa Wasu sojojin Nasu

Tun bayan kirkirar rundunar Operation FIRE BALL, mataimakiyar Operation LAFIYA DOLE ake ta samun nasara a Borno.

Cikin kankanin lokaci suka samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram 75, sai dai sojoji 3 sun rasa rayukansu, yayin da 4 suka samu raunuka – Sojoji 4 da suka samu raunukan suna asibitin sojoji, kuma da alama kwalliya tana biyan kudin sabulu don suna samun sauki Rundunar Operation Lafiya Dole tace mutane 78 duk da sojoji 3 suka rasa rayukansu a Borno, Dailytrust ta wallafa.

A wata takarda da kakakin rundunar soji, birgediya janar Benard Onyeuko ya saki a ranar Talata ya ce sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda masu yawa a jihar. Kamar yadda takardar tazo, “Tunda rundunar Operation FIRE BALL, mai taimakon Operation LAFIYA DOLE ta fara aiki, aka yi ta samun nasarori daban-daban a bangaren arewa maso gabas a kan miyagun ‘yan ta’addan nan na Boko Haram.

“Rundunar suna cigaba da gudanar da ayyukan babu dare ba rana. Ba don sadaukarwa da jajircewar sojojinmu ba da ba za a samu wadannan nasarorin ba.”

A cewarsa, yanzu haka an samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram 75 cikin dan kankanin lokaci. An samu nasarar kwato bindigogi 6, injinan gyaran bindigogi 4, bindiga kirar PKT daya, kananan bindigogi 10, abubuwa masu fashewa, bindigogi masu jigida da sauran miyagun makamai daga hannayensu.

Sai dai kananan sojoji 2 da wani babban soja sun rasa rayukansu, yayin da wasu 4 suka samu miyagun raunuka. Sojojin da suka samu raunukan na asibitin sojoji, inda ake kula da lafiyarsu kuma alamu na nuna kwalliya zata biya kudin sabulu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here