Osun: An Halattawa ɗalibai Mata sanya Hijabi a Jihar

Gwamnatin jihar Osun ta sanar da amincewa ɗalibai mata a jihar sanya hijabi a makarantu.

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar kula da harkokin ilimi a ma’aikatar ilimi ta jihar C. K. Olaniyan ta fitar, tana cewa ba a ware makarantu masu zaman kansu a sabon tsarin ba.

Ta kuma yi gargadin cewa matakin na da alaka da wani hukuncin kotu, don haka saɓa dokar na iya zama raina kotu.

Batun sanya hijabi a makarantu ya sha janyo ce-ce-ku-ce a wasu makarantu da ke Najeriya a shekarun baya-bayan nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here