Turkiyya: An ceto yarinyar da ta shafe Kwanaki a ƙarƙashin ƙasa

Magajin garin Izmir da ke kasar Trukiyya ya ce masu aikin ceto sun gano wata yarinya da ta shafe awanni casa’in da uku a ƙarƙashin ƙasa, bayan girgizar ƙasar da ta auku a yammacin ƙasar.

Mutane sun riƙa shewa da murna suna tsalle, yayin da aka ciro ta.

Mahukunta sun ce akalla mutane 100 ne suka mutu a girgizar ƙasar zuwa yanzu.

Har yanzu ba a gama tantance adadin mutanen da suka yi ɓatan dabo ba, amma masu aikin ceton sun duƙufa don neman waɗnda wataƙila ke raye.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here