MDD: Ta Girmama ‘Yar Najeriya a Matsayin ‘Yar sanda ta Shekara
An zaɓi wata ‘yar Najeriya a matsayin waɗanda aka grimama da samun kyautar lambar yabo ta ‘yar sanda ta shekara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Catherine Ugorji wadda ta yi aiki da tawagar MDD a ƙasar Mali, an zaɓe ta ne sakamakon jajircewarta wurin rage yawan aikata laifuka a ƙasar.
Read Also:
Jami’an MDD sun yabi ayyukan da ta aiwatar a rundunonin kiyaye zaman lafiya da kuma na filin daga.
“Taya murna ga Cif Sufuritanda Catherine Ugorji ta ‘yan sandan Najeriya da ke aiki da @UN_MINUSMA, wadda MDD ta zaɓa a matsayin ɗaya daga cikin mutum biyu da suka zo na biyu a kyautar ‘yan sanda na shekara,” a cewar ofishin MDD na Najeriya a shafinsa na Twitter.
“Ɗabi’un Catherine Ugorji sun jaddada ƙa’idojin aikin MDD.”