Cocin Owo: MURIC ta Bukaci Gwamnatin Jihar Ondo ta Biya Fulanin da Aka Kai wa Hari
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Musulunci MURIC ta bukaci gwamnan jihar Ondo ya biya Fulanin da aka kai wa hari a garin Owo diyya tunda gaskiya ta fito.
MURIC tayi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yanke hukunci ba tare da samun wani shaida ba dan kiyayyar da ake dashi ga wani kabila.
Kungiyar MURIC ta jinjinawa jam’ian tsaro bisa nasarar da suka samu wajen kama wadanda suka kai hari cocin Owo.
Jihar Ondo- Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Musulunci MURIC, a ranar Alhamis ta yi kira da a biya diyya ga Fulanin da aka yi ramuwar gayya akan su bayan harin da aka kai wa masu ibada a cocin St. Francis Catholic Owo a Jihar Ondo.Rahoton Daily Trust.
Read Also:
Legit.NG ta rawaito labarin yadda matasa suka kaiwa Fulani mazaunan garin Owo hari bisa zargin su suka kashe masu ibada cocin St. Francis.
Sai dai rundunar sojin Najeriya a ranar Talata ta ce an kama wadanda ake zargi da kai harin tare da bayyana sunayen wadanda ake zargin yan Ebira ne daga Okene a jihar Kogi.
MURIC, a cikin wata sanarwa da daraktan ta, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a jiya, Alhamis, ya bukaci gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da ya biya diyya ga Fulanin da aka kashe.
Sanarwar ya cigaba da cewa a biya wadanda suka yi asarar dukiyar su diyya kuma a samar da wani nau’i na agaji ga iyalan wadanda aka kashe a cikinsu.
MURIC ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yanke hukunci ba tare da kwakwarar shaida ba dan kiyayyar da ake dashi ga wani kabila.
Akwai masu laifi a cikin kowani kabila kamar yadda ake samun masu kirki a ko’ina.Kabilu ba sa aikata laifi mutane ne ke aikatawa inji MURIC
Kungiyar ta yabawa jami’an tsaro da kokarin da sukayi wajen bankado wadanda suka kai harin cocin garin Owo.