Ambaliyar Ruwa: Mutane 1,033 Sun Rasa Rayukansu a Pakisan 

Adadin wadanda suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan na ci gaba karuwa inda aka tabbatar da mutuwar mutum 1,033.

Hukumar agaji ta kasar ta ce karin mutum 119 ne suka rasu cikin awa 24.

A yanzu haka hukumomin Pakistan sun mika kokon bara ga kasashen domin tallafawa al’umma.

Rahotanni sun ce Firai ministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya sanar da bada tallafin dala miliyan 45 ga iyalan da bala’in ya shafa.

Mr Sharif ya ce mutane miliyan 33 ne ambaliyar ta shafa watau kashi 15 cikin 100 na yawan al’ummar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here