Mutum na Biyu da Yafi Arziki a Fadin Duniya
A shekarar 2020, Elon Musk ya maye gurbin Bill Gates, wanda yanzu haka, shine mutum na 2 a kudi, duk duniya.
Elon Musk, CEO din Tesla ne, yana da dukiya mai kimar dala biliyan 127.9, daidai da N48,755,480,000,000.
Tun 2017, Jeff Bezos ya doke Bill Gates, inda ya zama mai kudin kaf duniya, kuma har yau shi din ne.
CEO din Tesla, Elon Musk, yanzu haka ya maye gurbin Bill Gates, don yanzu haka shine mutum na 2 a kudi kaf duniya.
Duk da annobar coronavirus ta shekarar 2020 wacce ta girgiza tattalin arzikin duniya, amma dukiyarsa habaka tayi.
Read Also:
A cewar Bloomberg, yanzu haka Musk yana da dukiya mai kimar dala biliyan 127.9, wanda yayi daidai da N48,755,480,000,000.
Elon Musk ya riga ya maye matsayin Bill Gates, don yanzu haka shine mutum na 2 a kudi, duk duniya.
Bill Gates, wanda shine CEO din Microsoft Corporation, yana da dukiya. mai kimar dala biliyan 127.7, daidai da N48,679,240,000,000, Kudin da yakamata ya nunka hakan da a ce ba ya bayar da sadaka cikin shekarun da suka gabata zuwa yanzu ba.
Jeff Bezos ne ya maye gurbinsa a 2017, inda ya zama wanda yafi kowa dukiya a duniya, kuma har yanzu yana nan a matsayinsa. Gates ya bayar da kyautar fiye da dala biliyan 27 ta hanyar gidauniyarsa tun daga 2006 zuwa yanzu.