Karo na Biyu da Najeriya ta Fada Cikin Matsanancin Halin Tattalin Arziki
Alkallumar kiddigar abinda kasa ke samu sun nuna cewa Najeriya ta sake shiga matsin tatallin arziki a hukumance.
Matsin tattalin arzikin da kasar ta fada shine mafi muni da aka samu a kasar a shekaru 30 da suka shude.
Wannan shine karo na biyu da Najeriya ke fadawa matsin tattalin arziki a karkashin mulkin demokradiyya ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Read Also:
A hukumance, Najeriya ta fada cikin halin matsin tattalin arziki mafi muni cikin shekaru fiye da 30 kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
A cewar rahoton kiddidigar abinda kasar ke samarwa a shekara, GDP, ta Hukumar Kididdiga na Kasa, NBS, ta fitar a ranar Asabar, hada-hadar kasuwanci sun ragu da kashi 3.62 cikin 100 a watanni uku na karshen 2020.
Wannan shine karo na biyu da GDP din ke raguwa a jere tun matsin tattalin arzikin da kasar ta fada a shekarar 2016.Jumullan GDP din na watanni tara na farkon shekarar 2020 sun nuna alkallumar na -2.48%.
Lokaci na karshe da Najeriya ta samu irin wannan alkalluman GDP shine a shekarar 1987 a yayin da GDP din ya rage da kashe 10.8 cikin 100.