Nasarorin da Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya Samu a Cikin Kwanaki 100
Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya cika kwanaki 100 a kan kujerar shugabanci.
Domin murnar hakan, hukumar ta EFCC ta jero tarin nasarorin da Bawa ya samu a cikin wadannan kwanaki.
Shugaba Buhari ya nada Bawa a watan Fabrairu domin ya shugabanci hukumar bayan ficewar Ibrahim Magu.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta lissafa nasarorin da shugabanta, Abdulrasheed Bawa ya samu, domin murnar cikarsa kwanaki 100 a kan mulki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Bawa a watan Fabrairu domin ya shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa bayan ficewar Ibrahim Magu.
Ga jerin nasarorin da Bawa ya samu a cewar EFCC:
Read Also:
1. An kwato N6,142,645,673.38 (sama da Naira biliyan 6), $ 8,236,668.75, £ 13,408.00, da € 1,730.00, dalar Kanada 200, CFA374,000.00, ¥ 8,430.00 (Yen na kasar Japan)
2. An kwato motoci 25, jirgin ruwa guda biyar, babura biyu, shago daya, filaye shida, kafet daya, kayan lantarki 13, kadarori 30, masana’anta daya, gidan mai guda daya.
3. An kwato manyan kayayyakin man fetur 4. An tabbatar da hukunci 185 daga kararraki 367 da aka shigar a fadin ofisoshin shiyya.
Manyan ayyuka
1. Gyarawa da samar da kayan koyarwa na makarantar horarwa na hukumar, makarantar EFCC, Karu, Abuja.
2. Gyaran Ginin Hedikwatar Abuja, Benin, Gombe, Lagos, Fatakwal da Ofishin Shiyyar Uyo.
3. Gina Dakin Binciken na’ura na sabon sashin Leken Asiri da aka samar.
4. Gina karin ofisoshi a Benin, Enugu, Kaduna, Ibadan, Maiduguri, Sokoto da ofisoshin shiyyar Uyo.
5. Gina Cibiyar nazari na TOC a Ofishin Shiyyar Legas. 6. Raba motocin aiki da motocin daukar marasa lafiya da aka saya don inganta ayyukan hukumar, da sauran su.