Ɗaliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Jahar Ondo Sun Toshe Babbar Hanyar Akure-Ilesa

Akure, Ondo:- Wasu fusatattun ɗalibai na jami’ar fasaha ta tarayya dake Akure (FUTA), jahar Ondo, sun toshe babbar hanyar Akure-Ilesa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Rahoto ya nuna cewa ɗaliban sun ɗauki wannan matakin ne domin zanga-zangar kashe ɗan uwansu ɗalibi, wanda ya mutu a sanadin hatsari ranar Litinin da yamma.

Masu zanga-zangan sun bayyana cewa jami’an tsaron jami’ar FUTA sun ki buɗe musu kofa domin sukai ɗalibin asibiti bayan hatsarin.

Ɗaliban sun bayyana cewa wanda hatsarin ya rutsa da shi ka iya rayuwa inda an kai shi asibiti cikin lokaci.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa zanga-zangar ɗaliban ta jawo taruwar dandazon matafiya a kan hanyar.

Mai magana da yawun jami’ar FUTA, Mr Adengbenro Adebanjo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai Cikakken bayani zai biyo baya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here