NARD: Marasa Lafiya Sunyi Kira ga Gwamnati Akan ta Kawo Karshen Yajin Aikin Likitoci

Yau Kwana na biyu da Likitoci a Najeriya suka sake shiga yajin aiki.

Likitocin sun zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawuranta.

Marasa lafiya na jin jiki a asibitoci sakamakon wannan yaji.

Yan uwa na kwashe marasa lafiyansu daga asibitocin gwamnati yayinda yajin aikin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa (NARD) ya shiga kwana ta biyu.

Jaridar Sun ta bayyana cewa a asibitocin da ta ziyarta, Likitoci sun dauke kafa gaba daya kuma an bar marasa lafiya babu mai duba su.

Hakazalika an fadawa wadanda suka kawo sabbin marasa lafiyansu su tafi asibitoci masu zaman kansu.

Manyan Likitocin dake asibitocin sun yi karanci da yawa kuma ba zasu iya maye gurbin kananan likitocin da ke yaji ba.

Wasu marasa lafiya sun bayyanawa TheSun cewa suna kira ga gwamnati ta gaggauta kawo karshen wannan yajin aiki da Likitocin ke yi.

A asibitin FMC Abeokuta, jahar Ogun, malaman jinya sun fara sallaman marasa lafiyan dake jinya.

Wata Malamar jinya ta bayyana marasa lafiyan su biya kudin da asibiti ke binsu kuma su tafi gida ko su nemi wani asibitin.

Shugaban kungiyar Likitocin NARD na asibitin, Dr Busuyi Adebiyi, yace ya zama wajibi suyi biyayya ga uwar kungiya.

Yace:

“Har sai mun samu wani umurni na daban, zamu cigaba da yajin aiki. Wannan yajin aikin na kowa da kowa ne.”

Hakazalika, Likitoci a asibitin koyarwan jami’ar Ilori (UITH) sun bazama yajin aiki yayinda suke kira ga uwar kungiya ta wajabtawa gwamnati biyan bukatunsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here