ENDSARS: An ci Tarar Gidajen Talabijin na Channels, AIT, Arise
Read Also:
Muƙaddashin daraktan hukumar Farfesa Armstrong Idachaba, shi ne ya bayar da sanarwar tarar a yau Litinin a Abuja, inda ya ce za su biya tarar naira miliyan uku kowannensu.
An yaɗa hotuna da bidiyo na boge a tsakanin mako biyu da aka shafe ana zanga-zangar nuna ɓacin rai game da ayyukan rundunar ‘yan sanda a Najeriya, wadda aka yi wa laƙabi da EndSars – wato a rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami.
BBC ta bincika tare da bankaɗo gaskiya da ƙaryar wasu daga cikinsu a wannan labarin.
An ci tarar gidajen talabijin ɗin uku ne saboda “yaɗa hotunan da ba a tantance ba na harbe-harben da ake zargin an yi”.
Tun a baya, NBC ta gargaɗi kafofin yaɗa labarai da su yi taka-tsantsan wurin yaɗa hotunan da suka samu daga shafukan sada zumunta, tana mai cewa rashin tantance sahihancinsu ka iya jawo hatsaniya a ƙasa baki ɗaya