Yadda Wasu Ma’aurata Suka Azabtar da Karamar Yarinya

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wasu miji da mata, sakamakon kama su da laifin azabtar da karamar yarinya mai shekaru 8 da haihuwa.
Bincike ya nuna cewa, iyalan na azabtar da yarinyar ne, saboda ta shanye alawar N10 da suka sayo wa ‘yarsu mai shekaru 2 da haihuwa – Bidiyon yadda matar gidan ke dukan yarinyar bayan shanya ta a tsakiyar rana da kuma daure kafafunta, ya karade kafofin sada zumunta A ranar Litinin ne rundunar ‘yan sanda ta cafke wasu miji da mata, Mr da Mrs Philip Iboko, bisa zarginsu da azabtar da wata yarinya mai shekaru takwas da haihuwa. Rahotanni sun bayyana cewa an gano iyalan suna azabtar da yarinyar ne biyo bayan bullar wani bidiyo a yanar gizo da ke nuna yadda aka shanya yarinyar a rana bayan da aka daure kafafunta.
Yarinyar da miji da matar na zama a gida daya tsawon shekaru biyu, kuma anga matar a cikin bidiyon tana azabtar da yarinyar.
Iyalan da ke zama a karamar hukumar Izzi da ke jihar Ebonyi, sun huce haushin su kan karamar yarinyar bayan da ta shanye alawar N10 da suka sayowa yarsu mai shekaru biyu. Wata majiya ta tabbatar da cewa sai da makwaftan iyalan (Mr Chinedu da Mr Raymond) suka bayar da hakuri kana aka kwance yarinyar.
Makwaftan guda biyu, a cewar majiyar, sun kwance yarinyar suka cire ta daga cikin rana, kasancewar har ta galabaita sakamakon dukan da matar ta yi mata da kuma zafin rana. Duk wani yunkuri na jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi kan lamarin ya ci tura, kasancewar jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ba ta amsa wayar ta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here