Barkewar Rikici a Abakaliki

Rikici ya sake barkewa a yankin Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi

An tattaro cewa wasu bata gari sun sanya wa ofishin yan sanda da ke Onuebonyi wuta – A yanzu haka ance ana nan ana musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da bata garin Labari da ke zuwa mana, ya nuna cewa rikici ya sake barkewa a garin Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi yayinda ake ta ruwan harbi a sama. Rikicin wanda ya fara kimanin sa’a guda da ta gabata ya haifar da fargaba a birnin yayinda mazauna suka tarwatse ta kowani bangare, jaridar The Nation ta ruwaito. An tattaro cewa ba a san daga takamaiman wurin da harbe-harben bindigar ke fitowa ba.
Sai dai kuma rahoton yanar gizo ya nuna cewa wasu bata gari sun cinnawa ofishin yan sanda na Onuebonyi wuta. An kuma rahoto cewa jami’an yan sanda da sauran hukumomin tsaro na nan suna musayar wuta da bata garin a daidai lokacin kawo wannan rahoton

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here